Omar ya ce shawarwari sun gudana tsakanin sassan biyu a 'yan kwanakin baya, cikin adalci kuma bisa doka. Ya ce makasudin tattaunawar shi ne zakulo hanyoyin kawo karshen yakin kasar, wanda aka shafe tsawon shekaru 13 ana gwabzawa.
Rahotanni sun nuna cewa koda yake ana ta yada jita-jita harbe Mullah Mohammad Omar, sai ga shi gabanin karewar watan Ramadan, Omar din ya fidda sanarwa kamar yadda ya saba, yana mai cewa ana iya ganin cewa tsarin addinin Musulunci bai hana shawarwari ba, tare da yin hadin gwiwa cikin adalci da abokan gaba. Kuma a cewar sa bisa tsarin, an yarda da cimma yarjejeniya ta hanyar siyasa, ko kuma wasu hanyoyin na daban cikin adalci.
A ranar 8 ga watan ne gwamnatin Afghanistan, da wakilan kungiyar Taliban suka gudanar da shawarwari a karon farko tsakanin su a kasar ta Pakistan.(Fatima)