Yin Weimin ya isar da sakon taya murnar shugaban kasar Sin Xi Jinping ga Ghani da ya zama sabon shugaban kasar Afghanistan, kana ya bayyana cewa, kasar Sin tana maraba ga kasar Afghanistan da ta kafa gwamnatin hadin gwiwa da za ta kunshi dukkan al'ummun kasar, kana tana fatan kasar za ta samu hadin kan al'umma da zaman lafiya a karkashin jagorancin shugaba Ghani. Har wa yau kuma, kasar Sin za ta ci gaba da taimakawa kasar Afghanistan wajen sake shimfida zaman lafiya.
A nasa bangare,shugaba Ghani ya nuna godiya ga manzon musamman na shugaba Xi Jinping da ya halarci bikin rantsar da shi, kana ya bukaci Yin Weimin da ya isar da gaisuwarsa zuwa ga shugaba Xi Jinping. Ghani ya bayyana cewa, sabuwar gwamnatin sa tana dora muhimmanci ga zumunta da hadin gwiwa a tsakaninta da kasar Sin, tare da dangantakar dake tsakaninsu. Kasar Afghanistan tana fatan kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya gare ta wajen shimfida zaman lafiya, da taka muhimmiyar rawa wajen warware matsalolin da kasar Afghanistan ke fuskanta. (Zainab)