in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya taya sabon shugaban kasar Afghanistan murnar rantsuwar kama aiki
2014-09-30 10:01:48 cri
A jiya Litinin 29 ga wata ne, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya bayar da sanarwa ta bakin kakakinsa, inda ya taya Ashraf Ghani Ahmadzai murnar yin rantsuwar kama aiki a matsayin sabon shugaban kasar Afghanistan, kana ya taya Abdullah Abdullah murnar hawa kujerar babban jami'in siyasa na gwamnatin kasar.

Ban Ki-moon ya nuna cewa, kasar Afghanistan tana fuskantar kalubale, inda ya yi kira ga kasar da ta hanzarta kafa sabuwar gwamnatin da yin kokari tare da dukkan jama'ar kasar da nufin hada kan al'ummar kasar.

Haka kuma, Ban Ki-moon ya yi nuni da cewa, rantsuwar kama aikin da sabon shugaban kasar Afghanistan ya yi za ta shiga tarihi, kuma ya jaddada cewa, MDD za ta nuna goyon baya ga gwamnatin kasar da jama'arta a lokacin da ake kokarin kafa gwamnati da kuma a nan gaba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China