Mr. Carter ya bayyana hakan ne a yayin taron manema labaru da aka shirya a sansanin David, inda shugaban kasar ke hutu a wannan rana. Ya ce, domin tabbatar da tsaron kasar Afghanistan, kwamandan sojojin hadaka na Afghanistan da na kasashen waje, ya ba da shawarar tabbatar da aikin sojojin Afghanistan da yawansu ya kai dubu 352. Ya kuma yi imani da cewa, karancin sojoji a kasar zai kawo babbar hasara ga Afghanistan da sauran kawancen kasashen, don haka ya bayyana muhimmancin ci gaba da hadin gwiwa tsakanin Amurka da sauran kasashen duniya, wajen tabbatar da yawan sojojin da ake bukata a kasar cikin dogon lokaci.
Har wa yau, a gun taron manema labaru da aka gudanar, sakataren harkokin wajen Amurka John Forbes Kerry, ya sanar da cewa, za a bude wani sabon shirin hadin gwiwa tsakanin gwamnatocin Amurka da Afghanistan, don yin amfani da kudin agaji da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 800 wajen tantance, da sa kaimi ga cimma burin yin gyare-gyare ga gwamnatin Afghanistan, da kuma habaka ci gaban kasar. (Bako)