Kamfanin dillancin labaru na Reuters ya bayyana cewa, ofishin 'yan sandan lardin Khost da ke kasar ya ce, wani dan kunar bakin wake ne ya kai harin bam da dasa a cikin wata mota a wani wurin binciken ababan hawa da ke kudu maso gabashin kasar, harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 25, cikinsu har da mata da yara.
Ofishin 'yan sanda ya ce, maharin ya ta da bam din ne yayin da motoci da dama ke cikin layi a tashoshin binciken.
Kamfanin dillancin labaru na AP ya ce, wurin da aka kai harin bam din ba shi da nisa da sansanin sojojin Amurka da ke lardin Khost, wanda ke makwabtaka da kasar Pakistan. Sai dai sojojin Pakistan sun ce, babu wani sojin Amurka da ya ji rauni.
A wata sabuwa kuma, kafofin yada labaru na Afghanistan sun ce, a ranar Asabar hukumar leken asirin kasar ta tabbatar da cewa, sojojin saman Amurka sun harbe shugaban kungiyar IS mai kula da sashen Afghanistan da Pakistan Hafiz Saeed har lahira. Amma, kasar ba ta bayyana hakikanin abubuwa game da harin ba. Har yanzu, kungiyar NATO da sojojin Amurka ba su mayar da martani game da batun ba.(Bako)