Ofishin kwamitin ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwar da ya fitar a jiya ranar Lahadi.
A ranar Litinin ne dai wasu maharan kungiyar Taliban suka kai farmaki ginin majalissar dokokin kasar ta Afghanistan, lamarin da ya yi sanadiyyar hallakar fararen hula 5, baya ga wasu karin mutane 31 da suka samu raunuka.
An ce dan kunar bakin daya ya tada Bam a wata mota da yake tukawa domin baiwa sauran damar shiga ginin, lamarin da ya sabbaba rasuwar sa, kafin kuma daga bisani 'yan sanda su harbe sauran maharan su.
Lamarin dai ya auku ne lokacin da ake tsaka da jefa kuri'u a zaben ministan tsaron kasar.
Duk da cewa an fara ibadar Azumi a kasar ta Afghanistan, kungiyar 'yan Taliban a kasar ta ki amincewa da shawarar tsagaita bude wuta saboda shigowar watan na azumiRamadan, duba da yadda ta ke ci gaba da kaddamar da hare-hare. (Zainab)