Shugaba Ghani ya shaida ma wani taron da aka yi a fadar shi don murnar wannan rana cewa, rundunar tsaron Afghanistan yanzu suke da cikakken iko na wanzar da tsaro a fadin kasar daga wannan rana. Wannan wani rahama ne kuma yana taya daukacin 'yan kasar murna a kan wannan rana na tarihi.
Mika ragamar ikon rundunar tsaron ga hannun sojojin Afghanistan an fara shi ne tun watan Yuli na shekara ta 2011 kuma ya dauki lokaci har zuwa shekara ta 2014.
Yarjejeniyar amincewa a kan tsaro da matsayin rundunar NATO zai bada dama ga Amurka da NATOn su ajiye nasu sojojin a kalla 13,000 a Afghanistan.
A ranar har ila yau rundunar tsaron mai taimakawa na kasa da kasa na NATO zai kuma yi musanyar matsayi daga mai ba da jagoranci zuwa mai ba da taimako wanda zai mai da hankali wajen bayar da horo, shawarwari da taimakon sojojin Afghanistan.
Shugaba Ghani ya ce daga wannan rana shawarwari da sojojin Afghanistan da abokansu a kasa da kasa zai taimaka matuka.
Daga nan sai Shugaban kasar na Afghanistan ya mika godiya ga jami'an tsaron kasar a kan abin da ya kira nuna cewa su ainihin 'ya'yan Afghanistan ne. Kuma ana alfahari da su, an amince da su, kuma yana son daukacin al'ummar Afghanistan su ba su goyon baya.
Har ila yau Shugaban na Afghanisatn Mohammed Ashraf Ghani ya gode ma rundunar tsaron kasar bisa ga kokarinsu da sadaukar da kai. (Fatimah Jibril)