in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin kasar Sin ya yi kira da a cimma daidaito tsakanin sassan kasar Afghanistan
2015-03-17 15:35:02 cri

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Wang Min, ya ce kamata ya yi kasashen duniya su kara daukar matakan da suka dace da halin da ake ciki yanzu, inda gwamnati da jama'ar kasar Afghanistan suke taka muhimmiyar rawa, domin tallafawa shirin daidaita al'amura a kasar.

Game da batun Afghanistan, kwamitin sulhun MDD ya gudanar da wani taro a ranar Litinin, inda ya zartas da kudurin tsawaita wa'adin tawagar musamman ta MDD mai aikin wanzar da zaman lafiya a kasar ta Afghanistan ya zuwa ranar 17 ga watan Maris na shekarar 2016.

Yayin wannan taro, Mr Wang ya bayyana cewa ya kamata kasashen duniya su kara kwazo wajen aikin daidaita al'amura a kasar ta Afghanistan. Ya ce Sin na fatan taka rawar gani a wannan fanni, tare da aiki kafada da kafada da sauran bangarori daban-daban da batun ya shafa, da kuma samar da tallafi idan akwai bukata.

Dadin dadawa a jawabin nasa, Mr Wang ya yi kira ga mahukuntan kasar ta Afghanistan da su yi iyakacin kokarin bude sabon shafi na raya tattalin arzikin kasar, da kara hadin gwiwa da sauran kasashe a yankin da kasar take ciki, tare da kokarin cimma daidaito da kara shigar da MDD cikin batun kasar. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China