Sanarwar da ke wakiltar kungiyar Taliban da iyalan Mullah Omar na cewa, Mullah Omar din ya rasu sakamakon wata cuta.
A jiya ne dai, ma'aikatar harkokin wajen kasar Pakistan ta bayar da sanarwa cewa, sakamakon labarin da aka bayar na rasuwar shugaban kungiyar Taliban, shugabannin kungiyar Taliban ta kasar Afghanistan suka bukaci aka jikirta zagaye na biyu na shawarwarin zaman lafiya da aka tsara gudanarwa a yau Jumma'a a kasar Pakistan.
Game da wannan batu, bangaren Sin ya nuna amincewa da wannan mataki,kuma kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana a jiya cewa, Sin ta yi kira ga bangarori daban daban da abin ya shafa da su dora muhimmanci kan hadin kai da zaman lafiya na dogon lokaci a kasar Afghanistan, da ci gaba da sa kaimi ga samun sulhuntawa, wannan ya dace da moriyar jama'ar kasar da ta kungiyoyi daban daban na kasar, kana za ta taimaka wajen samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar. Hakazalika kuma, Lu Kang ya ce, Sin tana son ci gaba da yin kokari tare da bangarori daban daban ciki har da Pakistan wajen daidaita matsalar. (Zainab)