Wani babban jami'i mai kula da harkokin sakwannin sirri a kasar Somaliya ya ce wani mutum dan kasar Jamus mai asali a Somaliya ne ya kaddamar da hari kan otel din Al-Jazeera dake birnin Mogadishu fadar mulkin kasar Somaliya.
Jami'in da aka sakaye sunan sa, ya kara da cewa hukumar tsaron Somaliya, da hadin gwiwar sauran hukumomin kasa da kasa da MDD, na ci gaba da nazari game da harin. Ya ce mutumin da ake tuhuma da hannu cikin aukuwar harin na zaune ne a birnin Bonn dake yammacin kasar Jamus, bai kuma jima da dawowa Somaliya ba.
Idan ba a manta ba, a karshen makon da ya gabata ne aka kai harin kunar bakin wake da boma-bomai da aka dana cikin wata mota kan otel din Al-Jazeera, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla 15, ciki hadda wani mai gadi dake aiki a ofishin jakadancin kasar Sin a kasar ta Somaliya. (Amina)