Kwamitin ya ce, harin da kungiyar ta kai da ma duk wani irin aikace-aikacen ta'addanci da aka yi ba za su gurgunta aniyar kwamitin kan nuna goyon baya ga yunkurin zaman lafiya da neman sulhu a kasar Somaliya ba, haka kuma, kwamitin ya nuna juyayi ga wadanda suka rasa iyalansu cikin wannan hari, jama'a da kuma gwamnatin kasar, tare da fatan murmurewa ga wadanda suka jikkata cikin sauri.
Kana, kwamitin sulhu ya jaddada cewa, ya kamata a gurfanar da wadanda suka shirya da kuma aikata lafuffukan ta'addanci gaban kuriya, da kuma wadanda suka nuna goyon baya da samar da kudade gare su, a sa'i daya kuma, kwamitin ya sa kaimi ga kasa da kasa da su yi hadin gwiwa da gwamnatin kasar Somaliya kan aikin, bisa dokokin kasa da kasa da kuma kudurin kwamitin sulhu na MDD da abin ya shafa.
A ran 27 ga wata, an kai harin kunar bakin wake da kuma harin bindigogi a wani hotel dake birnin Mogadishu na kasar Somaliya, wadanda suka halaka mutane a kalla guda 10, yayin wasu suka jikkata.
Sa'an nan kuma, kungiyar Al-Shabaab ta sanar da daukar alhakin kai hare-haren. A cikin 'yan shekarun nan, kungiyar din mai kaifin kishin addinin musulunci ta yi ta kai wasu hare-hare a kasar Somaliya da ta Kenya. (Maryam)