A cikin wata sanarwa ta hadin gwiwwam MDD, ofishin IGAD na MDD, kungiyar tarayyar Turai EU, tawagar Afrika a Somaliya, Amurka, Sweden, Italiya, Habasha, Uganda da Turkiya dukkan su sun yaba ma al'ummar yankin tsakiyar Somaliyar saboda nasarar wannan taron da zummar sulhunta juna a garin Dhusamareb sakamakon fadan da ya auku a yankin.
Taron dai da aka fara kwanaki uku da suka gabata ya biyo bayan yarjejeniyar da aka rattaba ma hannu ne a watan Yulin bara a Somaliyar domin a kafa sabuwar jiha da zata kunshi kowa mai suna jihar tsakiya.
Wannan jihar zata zama ta uku tun da sabuwar kundin tsarin mulkin kasar ta fara aiki a shekara ta 2012. (Fatimah Jibril)