Ofishin 'yan sanda, Ismail Mohamed, ya bayyana cewa bam din ya tashi ne da nufin halaka jami'an diplomasiyyar UAE, inda ya kara da cewa fararen hula takwas da sojoji shida sun mutu a yayin harin, amma jami'an diplomasiyyar EAU sun tsirar da rayukansu.
Wani dan kunar bakin wake ya tada bam a cikin motarsa a yayin da ayarin motocin jami'an diplomasiyyar UAE ke wuce wa kusa da ofishin jakadancin kasar Turkiyya, in ji Mohamed. Muna iya tabbatar da cewa fararen hula takwas da sojoji shida ne suka mutu a yayin da wasu fararen hula biyar suka jikkata.
Gwamnatin Somaliya ta yi allawadai da wannan harin ta'addancin da babbar murya. Allah ya ji kan mamatan, kuma tana fatan samun sauki ga sojoji da fararen hulan da suka jikkata, in ji ministan watsa labarun kasar Somaliya, Mohamed Abdi Hayer. (Maman Ada)