Kakakin gwamnati Ridwan Haji ya ce Somaliya zata bada wannan kudin ga duk wanda ya bada bayanin yadda za'a samu ko kashe shugaban kungiyar Mohammed Diriye sannan kuma zata bada wani dalar 150,000 akan babban kwamandan kungiyar Mahad Karate
Haji yace Gwamnatin har ila yau ta ware kudi dala 100,000 akan duk wanda ya kamo ko yayi hanyar aka kamo sauran shugabannin su 9 na al-shabaab, ciki har da wanda ya shirya harin da aka kai a jami'ar Moi na garin Graissa dake Kenya abinda yayi sanadiyar mutuwar mutane 148 a makon jiya.
Shugaban kasar Somaliya Hassan Sheik Mohammed ya sanar a wannan makon cewar gwamnatin shi ta samar da wani mataki na yaki da kungiyar 'yan ta'addan sai dai bai bayyana wannan mataki ba ne.(Fatimah Jibril)