Obama ya ce halin da ake ciki a Somaliya na barazana ga tsaron kasar Amurka,da manufofinta na harkokin waje, don haka aka tsawaita wa'adin dokar-ta-baci, da takunkumin dake kan kasar wanda ya fara aiki tun a watan Afrilun shekarar 2010.
A shekarar 2010 ne dai shugaba Obama ya ba da umurnin sakawa wasu mutane, da kungiyoyin kasar ta Somaliya takunkumi, kana a watan Yulin shekarar 2012, ya sanar da hana fitar da charcoal daga cikin kasar. Daga baya kuma aka kara sakawa Somaliyar karin takunkumi, wanda ya shafi wasu mutane, da kungiyoyin kasar masu barazana ga wanzuwar zaman lafiya, da ayyukan ba da gudummawar jin kai.
Gwamnatin Obama ta bayyana cewa, fitar da charcoal daga kasar Somaliya na iya samar da kudin shiga mai yawa ga kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta Al-Shabaab dake kasar. (Zainab)