in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harin mayakan Al-shabaab ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 32 a Somaliya
2015-07-14 10:17:19 cri
Rahotanni daga Somaliya na cewa, kimanin mutane 32 ne suka hallaka, ciki har da mayakan Al-shabaab 25 yayin wata arangama tsakanin dakarun kungiyar tarayyar Afirka (AU) ko AMISOM a takaice da mayakan Al-Shabaab.

Magajin garin Rage Celle Yusuf Haji Mohamod wanda ya tabbatar da hakan ga manema labarai ya ce, fadan na ranar Litinin wanda ya faru a gundumar Rage Celle da ke kudancin kasar ta Somaliya ya kuma yi sanadiyar rayukan sojoji biyar da fafaren hula guda biyu.

Bugu da kari, mazauna yankin sun tabbatar da cewa, fadan da aka kwashe sa'o'i biyu da rabi ana gwabzawa, ya jikkata fararen hula da dama, baya ga wasu da suka bar gidajensu.

Sai dai bayanai daga yankin na cewa, yanzu al'amura sun daidaita bayan da dakarun gwamnati da na kungiyar tarayyar Afirka ko AMISOM suka yi nasarar fatattakar mayakan na Al-Shabaab.(Bello)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China