'Yan sandan kasar Somaliya sun bayyana a yau Litini 20 ga wata cewa, an kai harin bom kan wata motar MDD a yankin Puntland dake arewa maso gabashin kasar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 9 yayin da wasu 7 suka raunuka.
'Yan sanda sun ce, kila masu kai harin sun dasa bom a karkashin kujerar motar ne, kuma suka tada shi lokacin da motar ta shiga sansanin majalisar. Wadanda suka mutu sun hada da 'yan kasar Kenya biyu da masu tsaro na Somaliya 7.
Wakilin musamman na MDD mai kula da harkokin Somaliya Mr Nicholas Kay ya ba da jawabi a kan shafin yanar gizo ta twitter, don yin Allah wadai da harin. (Amina)