Wakilin shugaban kwamitin kungiyar a Somaliya kuma shugaban rundunar sojin kiyaye zama lafiya na AMISOM Mamman Sidikou yace babu wata rundunar sojin AU da suka janye daga wadannan wurare ko gauruwa wadanda ake kwace daga hannun al shabaab.
Mamman Sidikou yace AMISOM da Sojojin gwamnati na Somaliya wato SNA a yanzu haka suna kara jan damara da yin kwaskwarima na jibge sojojin su ta yadda zasu karfafa dabarun da suke dashi wanda a yanzu haka suka riga suka samu ikon kusan kashi 80% na tsakiyar kudancin kasar ya dawo hannun gwammati.
Shaidun gani ma ido sun ce sojojin tawagar AU sun bar manyan wuraren da suka hada da Owdhiigle da Qoryoole da kuma wassu kauyuka da suka hada da Tora-Torow, Mubarak da Bariire a yankin Lower Shabelle a daren ranar laraba sakamakom karuwan harin da kungiyar Al Shabaab kje kai masu.