Sojojin kiyayen zaman lafiyar da dama suka hallaka bayan da kungiyar al Shabaab ta afka ma garin da sojojin suke da sansani na Leego a kasar ta Somaliya a wannan rana ta Jumma'a.
An dai gano gawawwaki 50 wadansu su ma sun fita kamannin su, kamar yadda Guardian ta bayyana inda ta tabbatar da jiwo wassu bayanai daga bakin wadanda suka shaida hakan.
Babban magatakardar na MDD ya jinjina ma sojojin da suka rasa rayukansu saboda suna kan tafarkin samar da dawaumammen zaman lafiya ne ga Somaliya. Ya kuma mika sakon ta'aziya ga gwamnati da al'ummar kasar Burundi.
Mr. Ban daga nan sai ya jaddada kudurin majalissar na ci gaba da kokarin aiki da AMISOM da ita kanta kunyar AU domin goyon bayan al'umma da gwamnatin kasar Somaliya a kan tafarkin da suke bi na zaman lafiya. (Fatimah)