Sojojin gwamnatin Somaliya sun harbe dakaru 4 da suka kai hari a hukumar leken asiri ta gwamnatin kasar
Yau Lahadi 21 ga wata, wasu dakaru sun kai hari ga hedkwatar hukumar leken asiri da tsaron kasa ta Somaliya dake Mogadisho, babban birnin kasar. Sojojin gwamnatin sun harbe dakaru hudu a yayin musayar wuta da wadannan maharan, haka kuma jami'an tsaron kasar sun tabbatar da cewa babu wanda ya rasu ko jikkata cikin sojojin gwamnatin kasar.
Tuni dai, kungiyar Alshabaab ta kasar Somaliya ta sanar da alhakin kai harin. (Maryam)