in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi Allah wadai da harin da Al Shabaab ta kai a kasar Somaliya
2015-07-28 09:44:52 cri
A jiya ne babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya bayar da sanarwa ta hannun kakakinsa inda ya yi Allah wadai da harin da kungiyar Al Shabaab ta kai kan otel din Al-Jazeera da ke birnin Mogadishu na kasar Somaliya.

Sanarwar ta bayyana cewa, harin ya haddasa mutuwar mutane da raunatar mutum daya, baya ga wasu ofisoshin jakadancin kasashen waje da ke cikin otel din da suka lalace. Ban Ki-moon ya jajantawa iyalan mutanen da suka mutu a sakamakon harin,tare da fatan samun sauki cikin hanzari ga wadanda suka ji rauni .

Hakazalika kuma, sanarwar ta ce, wannan hari ba zai hana MDD da sauran kasashen duniya su taimakawa gwamnati da al'ummar Somaliya wajen samun makoma mai zaman lafiya ba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China