in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 43 sun rasu sakamakon harin kasar Yemen
2015-07-20 13:53:01 cri

Hukumar kiwon lafiya ta kasar Yemen dake gudu hijira ta ce kungiyar masu fafutuka ta Houthi, da dakaru magoya bayan tsohon shugaban kasar Ali Abdullah Saleh, sun gwabza fada a birnin Aden dake kudancin kasar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla 43, yayin da wasu 173 suka ji raunuka.

Kafar yada labarun yankin ta ce, dakaru masu dauke da makamai dake goyan bayan gwamnatin, da hadaddiyar kungiyar sojojin kasa da kasa karkashin jagoranci Saudiya, sun kwace birnin Aden daga kungiyar Houthi.

Wata sanarwa da gwamnatin ta bayar a ran 17 ga wata, ta sanar da maido da hedkwatar wucin gadi ta kasar a Aden bayan kwace birnin daga 'yan Houthi. Ya zuwa yanzu dai yawancin yankunan kasar na karkashin mallakar dakarun kungiyar ta Houthi, ciki hadda babban birnin kasar Sanaa.

Idan ba a manta ba, Houthi ta amshe birnin Sanaa da karfin tuwo a watan Satumbar bara, inda ta yiwa shugaban kasar Abd-Rabbu Mansour Hadi, da ministocinsa daurin talala a watan Jarairun bana. A kuma ranar 21 ga watan Fabarairu shugaba Abd-Rabbu Mansour Hadi ya tsere zuwa birnin Aden, ya kuma maida birnin hedkwatar kasar ta wucin gadi. Sai dai jim kadan da hakan, Abd-Rabbu Mansour Hadi ya yi gudun hijira zuwa Saudiya, bayan da kungiyar Houthi ta kutsa kai cikin birnin.

Dadin dadawa, a ranar 26 ga watan Maris, wasu kasashe ciki hadda Saudiya sun fara kaddamar da hare-hare ta sama, a wani matakin soja da aka yiwa lakabi da "Decisive storm" kan mayakan kungiyar ta Houthi. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China