Mr. Ban ya kuma yi kira ga daukacin bangarori daban daban da wannan rikici ya shafa da su halarci taron tare da ba da goyon baya da himma, ko a kai ga cimma nasarar da ake fata.
Cikin sanarwar, Ban Ki-moon ya kuma jaddada cewa, ya kamata bangarorin da za su halarci taron su hada da juna, su kuma sanya moriyar jama'ar kasar Yemen gaban duk wasu sauran bukatu. Kana ya yi kira gare su da su kiyaye yanayin siyasar kasar, domin tabbatar cimma nasarar shawarwarin.
Bugu da kari, Ban Ki-moon ya sake jaddada bukatar tsagaita bude wuta a sassan kasar, domin samar da damar shigar da taimakon jin kai ga jama'ar Yemen, matakin da kuma ka iya kaiwa ga bunkasa yanayin zaman lafiya, da gudanar shawarwarin da za a fara. (Maryam)