Wani jami'in tsaro da aka boye sunansa ya ce, a ranar Litinin, jiragen saman yaki na Saudiyya, da sauran kasashe masu mara mata baya, sun ci gaba da kai hare-hare ta sama ga sansanin soji a tsaunin dake yankin kudu maso yammacin birnin Sana'a, inda suka hallaka dakarun Houthi da sojojin gwamnati magoyon bayan tsohon shugaban Ali Abdullah Saleh a kalla 60. Haka kuma hare-haren sun rushe unguwannin fararen hula dake tsaunin, wanda hakan ya jikkata mutane a kalla 49.
Bisa kididdigar da ma'aikatar kiwon lafiya, da ma'aikatar kula da harkokin cikin gida ta kasar Yemen suka fitar, an ce, tun daga karshen watan Maris na bana, yakin basasa a Yemen, da hare-haren sama da ake kai wa kasar sun haddasa mutuwar mutane kimanin 700, tare da jikkatar wasu 3000.
An ce, rashin tsayayyiyar kananan gwamnatoci a kasar, ya sa abu ne mai wahala a iya tabbatar da kiyasin yawan mutanen da suka mutu ko suka jikkata, sabo da haka, yawan mutanen da suka mutu na iya zarce adadin da aka bayyana.(Bako)