Ban Ki-Moon ya yi wannan furuci ne, yayin da yake zantawa da manema labaru a jiya Laraba ranar 22 ga wata, inda ya ce ya yi na'am da dakatar da hare-hare ta sama da Saudiyya da ma sojojin hadakar kasashen dake goyon bayanta suka bayyana aiwatarwa a ranar Talata, kuma yana maraba da aniyar kasashen game da goyon bayan kudurin kwamitin sulhu na M.D.D, na sake farfado da yunkurin siyasa a Yemen, da kiyaye fararen hula, da tabbatar da samar da agajin jin kai.
Daga nan sai ya yabawa Saudiyya game da amincewarta ga bukatun M.D.D. wajen gaggauta ba da kudin tallafi da yawansu ya kai damar Amurka miliyan 274, domin taimakawa jama'ar kasar ta Yemen.
A wani ci gaban kuma, kakakin kwamitin tsaro a fadar White House ta Amurka Bernadette Meehan, ta fidda wata sanarwa, inda ta ce Amurka tana sa ran maye gurbin matakan soji da aka dauka a baya, da managartan shawarwari, a wani mataki na warware matsalar Yemen ta hanyar siyasa. (Bako)