in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Saudiyya da wasu sauran kasashe sun sake kai harin sama a Yemen
2015-05-18 20:52:46 cri
A yau Litinin 18 ga wata, wani jami'in gwamnatin Yemen ya bayyana cewa, bayan wa'adin tsagaita bude wuta na tsawon kwanaki biyar, Saudiyya da wassu sauran kasashen kawancenta sun sake kai harin sama kan dakarun Houthi 'yan darikar Shi'a a kasar Yemen.

Bisa kirar da Saudiyya ta yi, a daren ranar 12 ga wata da misalin karfe 11, ita da sauran kasashe sun dakatar da kai harin sama kan kungiyar Houthi, ta yadda kungiyoyin duniya ke iya jigilar kayayyakin agaji zuwa Yemen. A jiya lahadi 17 ga wata, a gun taro kan batun Yemen da aka shirya a birnin Riyadh, hedkwatar kasar Saudiyya, manzon musamman na MDD kan batun Yemen, Cheikh Ahmed ya yi kira ga bangarorin dake yin musayar wuta tsakaninsu da su tsawaita wa'adin tsagaita bude wuta, tare da komawa teburin shawarwari a fannin siyasa cikin lumana.

Bisa alkaluman da gwamnatin Yemen ta bayar, an ce, tun daga karshen watan Maris na bana zuwa yanzu, baki daya mutane sama da 1400 ne suka mutu, yayin da wasu sama da dubu 4 suka jikkata a sakamakon yakin basasa da kuma harin sama da Saudiyya da kasashen kawancenta suka kai wa kasar Yemen.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China