Hakan dai ya biyo bayan murabus da tsohon manzon musamman na MDD kan batun kasar ta Yemen Jamal Benomar ya yi a cikin wannan wata da muke ciki. Da yake bayyana nadin sabon wakilin a jiya Asabar, Mr. Ban ya kuma godewa wakilin mai barin gado, bisa kokarin sa na taimakawa jama'ar kasar Yemen, da kuma kwazon sa a aikin warware matsalar kasar da dai sauran su.
A wani ci gaban kuma, Mr. Ban ya nada Peter Jan Graaff daga kasar Holland, a matsayin sabon wakilin musamman kan batun cutar Ebola, kuma shugaban tawagar aikin gaggawa kan cutar Ebola na MDD, domin maye gurbin shugaban tawagar na yanzu Ismail Ould Cheikh Ahmed.
Cikin wata sanarwar da Ban Ki-moon ya fitar ta nadin jami'an, ya ce Peter Jan Graaff zai yi aiki kafada-da-kafada tare da manzon musamman na MDD game da cutar Ebola David Nabarro, da kuma gwamnatoci, da kungiyoyin da abin ya shafa. (Maryam)