Kana ofishin kakakin babban magatakardan MDD ya bayyana cewa, a wannan rana, hukumar jin kai ta MDD da abokanta na samar da taimakon jin kai sun fara tattara kudade cikin gaggawa a kasar Jordan.
Kuma za a yi amfani da kudaden wajen samar wa jama'ar kasar Yemen kayayyakin agaji, ruwan sha, abinci da kuma wuraren kwana da dai sauransu.
Kaza lika, bisa kididdigar da MDD ta yi, an ce, a halin yanzu, adadin mutanen kasar Yemen dake fama da karancin abinci ya kai miliyan 12, yayin da yara kimanin dubu 160 ke fama da karancin abinci, haka kuma, ba a da isassun makamashi da wutar lantakarki a wasu yankukan kasar, kana an dakatar da samar da ruwan sha a wasu yankunan kasar. (Maryam)