Stephane Dujarric ya bayyana cewa cikin sa'oi 24 da suka gabata, an ci gaba da kai hare-hare ta sama da boma-bomai, da kuma dauki-ba-dadi a jihar Saada dake arewacin kasar Yemen, lamarin da ya haddasa mutuwa, da raunatar mutane 13, ko da yake ba a iya tabbatar da hakikanin halin da ake ciki a yankin ba.
Hukumar kula da harkokin 'yan gudun hijira ta MDD ta bayyana cewa, wani jirgin ruwa mai dauke da kayayyakin gudummawa ya isa tashar jiragen ruwa ta Hoderdah dake kasar ta Yemen. Kuma da zarar an tsagaita bude wuta, za a kara yawan gudummawar da ake baiwa jama'a, ciki hadda raba tabarmin kwanciya, da barguna da nauyinsu ya kai ton 300, daga birnin Dubai zuwa kasar ta Yemen.
Ana dai sa ran wannan shiri na samar da gudummawa zai taimakawa mutane dubu 250 a kasar ta Yemen. (Zainab)