in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ba a cimma matsaya daya ba a shawarwari karo na farko kan batun kasar Yemen
2015-06-20 13:43:52 cri

An kammala shawarwari karo na farko kan batun kasar Yemen wanda MDD ta shawarta yin shi, kuma Wakilin musamman na MDD mai kula da batun kasar Yemen Ismail Ould Cheikh Ahmed ya kira wani taron manema labaru inda ya bayyana cewa, ko da yake ba a cimma matsaya daya cikin shawarwarin ba, amma yana da kyakkyawan fata a game da cimma tsagaita bude wuta a kasar ta hanyar yin shawarwari nan gaba.

Ismail Ould Cheikh Ahmed ya kara da cewea, halartar shawarwarin da babban magatakardan MDD Mr Ban Ki Moon ya yi wani matakin da ke nuna cewa, majalisar na dora babban muhimmanci kan wannan matsala. Yace ko da yake ana fuskantar kalubaloli daban-daban, duk da hakan bangarori daban-daban sun zauna tare sun tattauna tsakaninsu bisa shawarar Mr Ban Ki-Moon shi ma ya zama wani ci gaba da aka samu tare. Ya nanata cewa, Yemen na fuskantar rikicin jin kai mai tsanani, abin gaggawa shi ne bangarori daban-daban sun daina bude wuta ta yadda za a iya gudanar da ceton jin kai, musamman a lokacin Azumi.

Ban da haka kuma, Mr Ismail Ould Cheikh Ahmed ya ce, za a ci gaba da yin shawarwari irin wannan nan gaba. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China