Kungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwar da ta fitar a Lahadin nan.
A kwanan baya ma dai Saudiyan ta gabatar da makamancin wannan kira na kwanaki 5, domin samar da damar shigar da kayayyakin agajin gaggawa cikin kasar.
Game da kiran da Saudiyya ta yi a wannan karo, kungiyar ta Huthi ta nuna goyon bayan ta, da kuma burin ganin jama'ar kasar ta Yemen sun fita daga mawuyacin halin da suka fada.
Kaza lika, cikin sanarwar, kungiyar ta jaddada cewa za ta mai da martani idan har aka kai mata farkami, bayan amincewa da dakatar da bude wutar.
A daya hannun kuma, jam'iyyar GPC mai mulkin kasar ta Yemen, karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Ali Abdullah Sahel, ta fidda wata sanarwar dake nuna amincewarta da kiran na kasar Saudiya, tana mai cewa kiran zai iya samar da damar sassauta yanayin tashin hankalula, da jama'ar kasar ta Yemen ke fuskanta.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, tsagaita bude wuta na kwanaki biyar, ba za ta haifar da cikakken yanayi na zaman lafiya a kasar ba, sai dai hakan tamkar wani muhimmin mataki ne, wanda zai bude kofar shimfida zaman lafiya da lumana a dukkanin sassan kasar. (Maryam)