in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a yi shawarwari tsakanin bangarorin daban daban na Yemen
2015-06-15 11:28:03 cri
A jiya ne a birnin Geneva, manzon musamman na M.D.D.mai kula da batun kasar Yemen Ismail Ould Cheikh Ahmed ya ba da wata sanarwa, inda ya bayyana cewa, za a yi shawarwari a birnin Geneva tsakanin bangarorin daban daban na kasar Yemen karkashin shugabancin M.D.D. a a ranar 15 ga wata, bangarorin biyu da ke zaman doya da manja wato shugaban kasar Abde-Rabbuh Mansour Hadi da jagoran dakarun Houthi da za su tura wakilai don halartar taron. Kana kuma, M.D.D. ta yi kira ga bangarorin da abun ya shafa da su shiga cikin shawarwari ba tare da gindaya wani sharadi ba, don lalubo bakin zaren warware rikicin siyasar kasar.

Wannan shi ne karo na farko da bangarori daban daban na Yemen za su yi shawarwari karkashin shugabancin M.D.D.tun bayan da rikici ya barke a kasar. A ranar 14 ga wata da yamma ne, sakatare janar na M.D.D. Ban Ki-Moon ya isa birnin Geneva, inda ya gana da wakilin kwamitin hadin gwiwa kan kasashen Larabawa da ke yankin Gulf da jakadun kasashe 16 dake birnin Geneva.

A cikin sanarwar da ya bayar, Cheikh Ahmed ya ce, M.D.D. tana maraba da wakilin shugaban Yemen da ya halarci taron, inda ya yi kira ga bangarorin siyasa na Yemen da su yi shawarwari cikin aminci da girmama juna, don daddale wata yarjejeniyar da za ta kai ga warware rikicin kasar.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China