Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Tasnim na kasar Iran ya bayar, an ce, kasar ta tura wani jirgin ruwa mai bada tallafin jin kai zuwa kasar Yemen a jiya Lahadi 10 ga wata.
Wannan jirgin yana dauke da abinci da magunguna da sauran kayayyakin jin kai da nauyinsu ya kai ton 2500, sannan yana kuma dauke da likitoci 15, 'yan jarida 13 da wassu mutane 7 daga Amurka da Faransa da Jamus .
Jirgin wanda ya tashi daga mashigin teku na Bandar Abbas dake kudancin kasar Iran, ana sa ran zai isa Al hudaydah na kasar Yemen dake dab da bahar Maliya bayan kwanaki 10.
Tun daga karshen watan Maris, sojojin hadin gwiwa da kasar Saudiyya take jagoranta sun kai harin sama ga dakarun Houthi dake kasar Yemen, don haka mashigin teku na Aden dake dab da kasar Yemen ya kasance wani yankin da aka fi samun ayyukan soja. Amurka da Saudiyya sun nuna shakka ga kasar Iran kan ko zata yi jigilar tallafi ga dakarun Houthi ta hanyar jiragen ruwa. A farkon watan Afrilu, kasar Iran ta tura jiragen ruwan yaki guda biyu zuwa mashigin teku na Aden don yin aikin sintiri, lamarin da ya sanya kasar Amurka ta tura babbar jirgin ruwa mai saukar jiragen sama mai samfurin USS Theodore Roosevelt CVN-71 zuwa yankin nan take. (Zainab)