A safiyar ranar 15 ga wata, a birnin Geneva, Ban Ki-moon ya gana da wakilan gwamnatin Yemen da za su halarci shawarwari a Geneva, inda bangarorin suka yi tattaunawa mai gamsarwa. A gun taron manema labaru bayan taron, Ban Ki-moon ya ce, daga watan Mayu na bana zuwa wannan lokaci, rikicin kasar ta Yemen ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kimanin 2600, rabi daga cikinsu fararen hula ne, abin da ke nuna mawuyacin hali, da kasar ta Yemen ta shiga.
Ban Ki-moon ya ce, hakkin bangarorin da abun ya shafa na Yemen shi ne su kawo karshen yake-yaken, da fara yunkurin zaman lafiya da sulhuntawa, a sa'i daya kuma, su ma kasashen duniya na da hakkin ba da goyon baya ga wannan yunkurin.(Bako)