Babbar jam'iyyar adawa ta kasar ta mai da martani a wannan rana cewa, ko da yake an yanke shawarar dage lokacin zaben, amma za ta ci gaba da kaurace wa zaben da za a yi, saboda a cewarta akwai rashin yanayin adalci da aminci wajen yin zaben.
Burundi dai ta gudanar da zaben majalisar dokoki da na jihohi a ran 29 ga watan Yuni, daga baya kuma hukumar zabe mai zaman kanta na kasar ya sanar a daren ran 7 ga wannan wata da muke ciki cewa, jam'iyya mai mulki ta samu kujeru 77 daga cikin 100 na majalisar dokokin. Ban da wannan kuma, Burundi za ta yi zaben 'yan majalisar dattawan kasar a ran 24 ga wata. (Amina)