Bisa tsarin mulkin kasar ta Burundi, al'ummar kasar na zabar shugaban kasar, wanda ke jagorantar kasar a tsahon wa'adin shekaru 5, kana shugaba mai ci na iya kasancewa kan karagar mulkin kasar a karo biyu.
Majalissar dokokin kasar Burundi ce dai ta amince da shugaba Nkurunziza ya jagoranci kasar Burundi a shekarar 2005. Kana ya sake samun damar zarcewa bayan lashe babban zaben kasar na shekarar 2010. A kuma ranar 25 ga watan Afrilun da ya gabata, jam'iyyar sa ta FDD ta sake bayyana Nkurunziza a matsayin dan takarar ta a karo na uku, matakin da jam'iyyar adawar kasar ta ce ya sabawa doka.
Sai dai duk da kasancewar Nkurunziza ya jagoranci Burundi har karo biyu, magoya bayan sa na ganin shugaban na da ikon sake tsayawa takara a wannan karo, duba da cewa ya hau karagar mulkin kasar a shekarar 2005 ne ta hanyar amincewar majalissar dokoki, ba wai ta hanyar kada kuri'un al'ummar kasar ba. (Zainab)