Kanar Baratuza kamar yadda yayi bayani a cikin wata sanarwar da ya fitar yace babu wani abu kamar haka da ya faru kuma kan su a hade yake. Abin da mutane suke ji jita jita ne kawai.
Yace ana ta jita jita a cikin babban birnin Bujumbura cewa wai wassu sojoji sun ki amincewa da korar tsohon ministan tsaron Manjo Janar Pontien Gaciyubwenge.
A ranar litinin, Emmanuel Ntahomvukiye wanda bai taba samun horon soji ba, an nada shi ministan tsaron kasar, 'yan kwanaki kadan bayan wani yunkurin juyin mulki da yaci tura akan shugaban kasar Pierre Nkurunziza wanda yake takarar shugabanci a karo na uku a zaben da za a yi a watan gobe. (Fatimah)