Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya umarci Abdoulaye Bathily daga kasar Senegal, da ya kasance mai shiga tsakani a tattaunawa ta gaba tsakanin bangarorin kasar Burundi.
Hakan dai ya biyo bayan aje aiki da wakilin musamman na MDD mai lura da yankin manyan tafkunan Afirka Said Djinnit ya yi, bayan da 'yan adawar kasar Burundin suka zarge shi da goyon bayan tsagin gwamnati.
Cikin wata sanarwa da kakakinsa ya fitar a jiya Lahadi, Mr. Ban ya ce a wannan gaba da zabukan kasar ta Burundi ke kara matsowa, ya zama wajibi daukacin masu ruwa da tsaki a siyasar kasar su dauki dukkanin matakan da suka wajaba, na kawo karshen sabanin dake tsakaninsu. Mr. Ban ya kuma bukaci da a koma teburin shawara, domin cimma nasarar gudanar babban zaben kasar cikin kyakkyawan yanayi, wanda kuma sakamakonsa zai samu karbuwa ga kowa.
A baya dai an yi shirin ci gaba da tattaunawa cikin makon da ya gabata, bayan bude shawarwarin a ranar 5 ga watan Mayun da ya shude, kafin daga bisani 'yan adawar kasar su bukaci sauya jami'in dake shiga tsakani.
Yanzu haka dai muhimmman batutuwan da ake zaton da su mamaye ajandar zaman na gaba, sun hada da batun halascin takarar shugaba Pierre Nkurunziza a karo na uku, da kuma yunkurin kawo karshen zanga-zangar dake aukuwa a kasar. (Saminu Alhassan)