Burundi: Jam'iyyar FNL dake kusa da gwamnati ta janye yardarta ga mai shiga tsakani
Jam'iyyar FNL, jam'iyyar da ke kusan gwamnatin Burundi ta janye yardarta ga mai shiga tsakani na kasa da kasa domin sasanta 'yan kasar Burundi, Abdoulaye Bathily, tare da bayyana cewa wannan matsayi ya kamata a mika shi ga gamayyar tattalin arzkin gabashin Afrika (EAC). Shugaban jam'iyyar FNL, Jacques Bigirimana, a cikin wata sanarwa da aka karanta a gidan rediyon kasar Burundi ya jaddada cewa kungiyar EAC ita kadai ke da hurumi da karfin fahimtar fiye da sauran halin da kasar Burundi take ciki. Ana zargin Abdoulaye Bathily da nuna son kai a cikin aikinsa na mai shiga tsakani.
Kawancen jam'iyyun adawa (POPO) sun sanar a ranar Asabar a gidan rediyon kasa a cikin wata sanarwa cewa suna adawa da yin alla wadai da yadda aka gudanar da zabe a ranar 29 ga watan Yunin shekarar 2015, kuma daga bisani suka bayyana cewa ba za su shiga duk wasu hukumomin da suka biyo bayan wannan zabe ba. Muna jaddada cewa duk wani sakamakon da zai biyo bayan wannan magudin zabe, mambobinmu ko guda bai shiga a wadannan hukumomi ba, tare da yin kira ga 'yan kasa da gamayyar kasa da kasa da su yi watsi da sakamakon wannan zabe, in ji kawancen POPO. (Maman Ada)