in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da zaben 'yan majalisun dokoki a kasar Burundi
2015-06-30 10:07:05 cri

A jiya ne sama da mutane miliyan 3.8 suka fito kada kuri'a a kasar Burundi duk da boren 'yan adawa na neman a dage zabukan kasar saboda yanayin da ake ciki a kasar.

Rahotanni daga Bujunbura, babban birnin kasar na cewa, an bude cibiyoyin ka da kuri'a a makare sakamakon wani rikici da ya barke a daren ranar Lahadi. Bugu da kari wani ya tayar da gurneti a kusa da wata cibiyar kada kuri'a a garin Kibago da ke kudancin lardin makamba, lamarin da ya kawo hargitsi na dan wani lokaci.

Har ila nan dan dakatar da zabe a tashar kada kuri'a da ke Kiremba da ke gabashin lardin Bururi bayan da wani soja ya yi harbi bisa kuskure, ko da ya ke al'amura sun daidaita daga bisani.

Kimanin 'yan majalisun dokoki 100 da kansilolin kananan hukumomi 1,785 ake saran zaba a zaben na jiya Litinin da a baya 'yan adawar kasa su yi shekar cewa, ba za su halarta ba. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China