Sanarwar ta ce, wakilan fararen hula, da na gwamnatin kasar, da na jam'iyyu daban daban, da na kungiyoyin addinai sun halarci wannan taro, tare da wakilai daga MDD da kungiyar AU da ta EAC da dai sauransu. Ban Ki-moon ya nuna yabo ga ci gaban da aka samu bisa shawarwarin, kuma ya nanata cewa, MDD za ta ci gaba da nuna goyon bayanta ga Burundi da ma yankin.
Bisa alkaluman da hukumar 'yan gudun hijira ta MDD (UNHCR) ta bayar, an ce, daga watan Afrilun bana zuwa yanzu, baki daya kimanin mutanen Burundi dubu 100 sun yi gudun hijira zuwa Rwanda, Tanzania, Kongo Kinshasa da sauran kasashe makwabta. A jiya hukumar UNHCR ta yi kira da a kara ba da taimakon jin kai ga wadannan 'yan gudun hijira na Burundi. Dadin dadawa, a wannan rana, babban jami'in hukumar UNHCR, Antonio Guterres ya ba da sanarwar nuna bakin cikinsa ganin halin da 'yan gudun hijira suke ciki, kuma ya nuna godiyarsa ga wadannan kasashe makwabtan Burundi da su tsugunar da su yadda ya kamata. Ya yi kira ga kasashen duniya da su nuna goyon baya ga shirin ba da agajin jin kai yadda ya kamata.(Fatima)