A cikin sanarwar, Ban Ki-moon ya bukaci bangarori daban daban na kasar Burundi da su hada kai da Said Djinni, manzon musamman na MDD mai kula da harkokin manyan tafkuna na Great Lakes da ke gabashin Afirka, ta yadda za a sake komawa kan teburin shawarwari tsakanin sassan kasar. Haka zalika Ban ya bayyana fatansa na ganin an dauki matakai nan take bisa wani shirin da aka cimma matsaya a kai.
Ban da haka, Ban ya nuna farin cikinsa game da sanarwar da aka gabatar wajen taron kolin kungiyar raya gabashin Afirka da ya gudana a ranar 31 ga watan Mayu, kana ya bukaci a aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma cikin sauri, don samar da yanayin da ya dace a kokarin gudanar da babban zabe cikin kwanciyar hankali da gaskiya a Burundi, wanda kuma zai kunshi bangarori daban daban na kasar. (Bello Wang)