Kwamitin sulhu na M.D.D. ya ba da wannan sanawa ne a jiya Lahadi, yana mai janjantawa dangin mamacin, tare da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata sakamakon aukuwar harin. Kaza lika kwamitin ya bukaci gwamnatin Burundi da ta gurfanar da wadanda suke da hannu cikin kisan Feruzi gaban kuliya.
Har wa yau sanarwa ta ce kwamitin sulhun M.D.Dr ya yi kira a bangarorin da rikicin siyasar kasar Burundi ya shafa da su kai zuciya nisa, a sa'i daya kuma, ya bukaci gwamnati da ta dauki kwararan matakai na hana aukuwar tashe-tashen hankula a kasar.
A daren ranar 23 ga watan nan ne dai wani mahari ya harbe Zedi Feruzi har lahira, kana wani mai tsaron lafiyarsa shi ma ya rasa ransa a harin, baya ga wasu mutanen da suka jikkata kuma maharin ya tsere.
Feruzi jigo ne daga 'yan adawa da manufar shugaba Pierre Nkurunziza, ta tsayawa takara a karo na uku, tun kuma daga ranar 26 ga watan Afrilun da ya shude ake ci gaba da zanga-zangar kin jinin gwamnatin a kasar ta Burundi, lamarin da ya hallaka mutane sama da 25. (Bako)