in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An hallaka shugaban jam'iyyar adawa a kasar Burundi
2015-05-24 17:02:58 cri
Da yammacin jiya Asabar 23 ga watan nan ne wani dan bindiga ya harbe shugaban jam'iyyar adawar kasar Burundi Zedi Feruzi har lahira.

Zedi Feruzi wanda ke jagorantar jam'iyyar UPD-Zigamibanga, na shugabantar zanga zangar adawa da batun takarar shugaban kasar ta Burundi Pierre Nkurunziza, wanda ke neman a sake zabensa a karo na uku.

Jam'iyyar UPD-Zigamibanga dai bangare ce ta hadaddiyar kungiyar masu fatan ganin an gudanar da gyare-gyare ga tsarin demokuradiyya a kasar, wadda ta hada da wasu jam'iyyun adawa, da kuma kungiyoyin jama'a.

Tun dai bayan zanga-zangar da ta gudana a ranar 26 ga watan Afrilun da ya shude ya zuwa yanzu, sama da mutane 25 sun rasa rayukansu, a tashe-tashen hankula dake aukuwa a kasar ta Burundi. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China