A cikin wata sanarwa Shugaba da aka amince da shi, mambobin kwamitin su 15 sun bayyana matukar damuwar su game da yanayin tsaro da siyasa a Burundin ganin matsowar babban zabe na Shugaban kasar da na majalissar dokoki.
Kwamitin tsaron ta yi taron gaggawa ne a kan Burundin a ranar Jumma'an nan da rana inda jakadan kasar ta Burundi a majalissar Albert Shingiro ya shaida mata cewa za'a gudanar da zaben kamar yadda aka rigaya aka shirya a ranar Litinin, duk kuwa da kiran da Babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon ya yi a safiyar Jumma'a ga mahukuntar kasar na kara jinkirta zaben.
Rahotanni na nuna cewa jam'iyyun adawa za su kaurace ma zaben shugaban kasar Pierre Nkurunziza wanda yake neman komawa a karo na 3 abin da ya saba ma adadin na sau 2 da kundin tsarin mulkin kasar ta tanada. (Fatimah)