Kakakin gwamnatin Burundi Philipe Nzobonaliba, ya ce, dage zaben da wata guda da rabi kamar yadda EAC ta ba da shawara, zai baiwa 'yan adawa dake korafin karancin lokaci damar sake shiri na shiga zaben.
A jiya Lahadi ne dai shugabannin kasashe manbobin kungiyar ta EAC suka gudanar da taron gaggawa a birnin Dar es Salaam na kasar Tanzaniya.
Sanarwar bayan taron dai ta nuna matukar damuwar shugabannin kasashe mambobin kungiyar, game da halin kunci da ake ciki a kasar Burundi, suna masu kira da a dage zabubbukan kasar da tsawon wata guda da rabi.
Haka kuma, sanarwa ta yi kira ga bangarorin daban-daban dake kasar ta Burundi da su kai zuciya nesa, su kuma kauracewa tada hargitsi.
Shugaba Nkurunziza bai halarci taron na EAC ba, sai dai rahotanni sun ce, ya tura tawagar ministocin sa a matsayin wakilan kasar sa. (Bako)