Sanarwar ta ce, da babbar murya ne, kwamitin ya yi allawadai da harin da kungiyar adawa ta kai a jihar Upper Nile a ran 20 ga wata, da kuma martani da sojin gwamnati suka mayar a ran 23 ga wata. Kwamitin ya kalubalanci bangarorin biyu da su nace ga yarjejeniyar da suka daddale a baya, kuma ya bukace da su daina nuna kiyayya tsakaninsu da koma teburin shawarwari yadda ya kamata.
Ban da haka kuma, kwamitin ya nanata cewa, ya kamata, an yankewa wadanda suka karya hakkan bil'adama da sabawa dokar jin kai ta kasa da kasa hukunci, tare da nuna yabo ga sanarwar da kungiyar raya kasashen gabashin Afrika IGAD ta bayar na maido da shawarwari tsakanin bangarorin biyu na Sudan ta kudu a ran 30 ga watan Yuli da ya gabata.
Dadin dadawa, a cikin wata sanarwa ta daban da kwamitin ya bayar a wannan rana, an nuna matukar damuwa ga karancin abinci da Sudan ta Kudu ke fuskanta yanzu, ana ganin cewa za a fama da yunwa a kasar. (Amina)