Mr. Wang ya kara da cewa, matakin zai yi amfani kwarai a fannin kiyaye tsarin hana yaduwar makaman nukiliya a duniya, baya ga samar da zaman lafiya da zaman karko a yankin Gabas ta tsakiya. Ya ce kasar Sin za ta ci gaba da shiga shawarwarin warware batun nukiliyar ta Iran daga duk fannoni kuma cikin dogon lokaci yadda ya kamata.
A jiya Talata ne aka gudanar da taron kwamitin sulhun M.D.D., inda aka saurari rahoton da kwamitin kakaba takunkumi ga kasar Iran na M.D.D. ya mika. A cikin jawabinsa Wang Min ya ce kasar Sin tana ganin cewa, dukkanin bangarorin da abun ya shafa na da alhakin gudanar da kudurin da kwamitin sulhun M.D.Dr ya tsaida, game da kakaba takunkumi ga Iran cikin tsanaki. Sai dai ya ce takunkumin ba zai zama makasudin M.D.D. ba, domin kuwa kamata ya yi a sanya himma wajen warware batun nukiliyar Iran ta hanyar siyasa. (Bako)