Tashar gidan telabijin ta kasar Iran wato "Press TV" ta labarta cewa, shugaba Rouhani ya yi wannan tsokaci ne a Tabriz dake arewa maso yammacin kasar, yana mai cewa gwamnatinsa za ta bi umarnin da shugaban majalisar kolin kasar Ayatollah Khamenei ya gabatar a ranar Laraba, cewa ba za su amince da wata yarjejeniya, da za ta yarjewa kasashen waje samun sirrin Iran a fannonin kimiyya da aikin soja ba.
A cewar Rouhani, gwamnatin kasar za ta bi umarnin Khamenei sau da kafa, yayin da tawagar kasar mai halartar shawarwarin da ake gudanarwa za ta tsaya kan matsayinta na cewa ko kadan, ba za ta yi rangwame a wannan fanni ba.
Kafin hakan, tawagar Iran ta riga ta bayyana matsayinta na bukatar soke takunkumin da aka sanya wa kasar, da neman amincewa kasar Iran ci gaba da nazarin fasahar nukiliya, da aikin tace sinadarin Uranium. (Bello Wang)