Mr. Cheng ya ce bisa tsarin da ake kai, sakamakon zaman da masu ruwa da tsaki suka yi a kasar Switzerland cikin watan Afirilun da ya gabata, yanzu haka ana maida hankali ga cimma yarjejeniyar karshe, kafin wa'adin da aka gindaya, wato nan da karshen watan nan na Yuni.
A cewarsa muhimman batutuwan da ake fatan warwarewa dai sun hada da dage takunkumin da aka kakabawa kasar ta Iran.
A daya hannun kuma, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi, ya shaidawa kamfanin dillancin labaru na APA cewa, kasarsa na fatan cimma matsaya, wadda za ta marbata 'yancin ta, tare da dage takunkumin da aka sanya mata.
Kafin hakan dai Mr. Araqchi ya zanta da shugaban hukumar kula da makamashin Nukiya ta MDD Yukiya Amano, wanda ya dade yana bukatar Iran din ta yi bayani filla-filla, game da shirinta na mallakar makaman nukiliya, ko da yake Iran din ta kafe cewa ba ta da manufar mallakar makaman na Nukiliya. (Saminu Hassan)